EFCC: Matasa sun Fara Zanga Zanga kan Kama Mutum 127 da Ake Zargi da Damfara
- Wasu fusatattun matasa sun yi zanga-zanga a jihar Ondo inda su ka rufe hanyoyi wanda ya kawo tsaiko wajen zirga-zirgar ababen hawa a Akure
- Matasan na zanga-zanga domin nuna rashin jin dadi kan yadda jami'an hukumar EFCC su ka kai samame wani gidan rawa tare da cafke matasa da dama
- Hukumar EFCC na zargin matasan da damfara ta kafar intanet, amma ma su zanga-zangar da su ka je har fadar gwamnati na ganin karya kawai aka yi masu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ondo-Wasu matasa a Akure, da ke jihar Ondo sun gudanar da gagarumar zanga-zanga suna neman hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta gaggauta sakin wasu da ta kama bisa zargin damfara da kafar intanet.
Gwamanti ta fadi yadda za ta kwato bashin da ta rabawa mutane a lokacin Corona
A wani samame da ta kai gidan rawa, hukumar EFCC ta kama akalla matasa 127 da ake zargi su na damfarar jama’a ta kafar intanet.
Nigerian Tribune ta wallafa cewa matasan na cewa EFCC ta kama matasan ne bisa zargi, amma sam ba ta da tabbacin wadanda ta kama din ‘yan ‘yahoo’ ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa sun nemi sakin wadanda aka kama
Matasan da suka yi zanga-zanga a Akure babban birnin jihar Ondo sun nemi gwamnati ta kawo karshen hukumar EFCC saboda takurawa jama’a da ta ke yi.
Matasan na zanga zangar kwashe wasu mutane da aka yid aga gidan rawa bisa zargin damfarar jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.
Matasan sun rike kwalaye dauke da rubutu suna neman gwamnati ta kawo karshen hukumar EFCC da ma neman a sama masu aikin yi.
Kano: Hukumar yaki da rashawa ta fara binciken zargin almundahana a tallafin gwamnati
Masu zanga-zanga sun yi tattaki har zuwa ofishin gwamnatin jihar da ke Alagbaka inda su ka rufe hanyoyi tare da kawo tsaikon zirga-zirga.
An cafke mata bisa zargin zamba
A wani labarin kun ji cewa hukumar EFCC ta kama wata mata mai suna Blessing da surukarta bisa zargin zambar kudin wasu filaye guda uku a Portharcourt.
Jami'an EFCC sun kama matan ne a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers suna kokarin zambatar Senibo Richmond Opusunju, tuni hukumar ta grufanar da su gaban kotu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboN3gJZmpqecn2K6osDArJhmq6Wjeqet0Zpks5menK5uxsCnnpqqXaCurq2MsJidmZ6Zrm6typ5ks5minLZusMBmm5qllpa%2Fons%3D